Labarai

Rikici tsakanin kabilun Tiv da Jukun yana damu na – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rikicin kabilun Tiv da Jukun na jihohin Benue da Taraba dake arewacin Najeriya yana damunshi matuka.

Sanarwarta fito a wata takarda mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu.

Rikici tsakanin kabilun biyu ya dade yana jayo asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa,wanda yake haifar da zaman dar-dar, rarraba kan al’ummar yankin hadi da kin yadda da juna.

Sashin Hausa na Muryar Amurka ta rawaito cewa; Sanarwar ta kara da cewa, tini dai shugaba Muhammadu Buhari ya fara shirin kafa kwamitin masu ruwa da tsaki don yi binciken kwa-kwaf na ganin an gano musabbabin rikice rikicen tsakanin kabilun dama sauran al’ummar Najeriya.

Sanarwar tace kwamitin zai fi mayar da hankali kan rikicin kabilun guda 2 wanda rikicin ya kara yin tsamari a ‘yan kwanakinnan.

DABO FM tabbatar da sanarwar dai ta ce, kwamitin zai yi aiki tare a ofisoshin addinai musamman kungiyar addinin Kiristanci ‘CAN’ da Majalissar dake kula da addinin Islama da kungiyoyin ‘yan kasuwa, manoma da mafarauta.

Kwamitin bazai tsaya nan ba, zai hada har da jami’an tsaro, jami’an kananan hukumomi da na jiha.

Muryar Amurka ta rawaito; “Shuguba Buhari na da yakinin cewa, banbance-banbancen al’umomi da Najeriya ke da shi, shi ne ginshikin hadin kanta da zaman lafiya da ci gabanta.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin Tarayya ta ba da aikin Hanyar da akai shekara da shekaru ana nema

Rilwanu A. Shehu

Nan gaba duk dan takarar shugaban kasar da yazo yana muku kuka to kuyi ta kanku -Shehu Sani

Muhammad Isma’il Makama

Hotuna: An raƙashe a taron bikin canza sunan Buhari zuwa Sulaiman da wani Bakatsine yayi

Muhammad Isma’il Makama

Shugaba Buhari zai bar Najeriya zuwa kasar Chadi a safiyar yau

Dabo Online

Ko Sheikh Zakzaky zai warke a kasa da kwanaki 1416 da suka ragewa Buhari da El-Rufai?

Dabo Online

Zuwa ga Shugaba Buhari: Idan kai mai gaskiya ne, ka tonawa barayin kusa da kai asiri – Gwamnan Akwa Ibom

Dabo Online
UA-131299779-2