Home LabaraiRikici ya barke a Majalissar Dokokin jihar Jigawa: An dakatar da ‘Yan Majalissu Biyu

Rikici ya barke a Majalissar Dokokin jihar Jigawa: An dakatar da ‘Yan Majalissu Biyu

by Rilwanu A. Shehu
0 comments

Majalissar Dokoki ta jihar Jigawa ta fara daukar dimin rikici a zaman ta na yau Talata, 24 na watan Satumba.

Kakakin majalissar, Hon. Idris Garba Jahun, ya sanar da dakatar da ‘yan majalissu masu wakiltar Ringim da Gumel, daga karba duk kan wani Albashi ko Alawus a Majalissar.

Akwai zargin tsohuwar gaba a tsakanin kakakin Majalissar da kuma su wadancan ‘yan Majalissu guda biyu tun a baya.

‘Yan Majalissar dai, sun yi kaurin suna wajen adawa da salon mulkin kakakin Majalissar, wanda hakan ya kai ga tsige shi kakakin Majalissar a baya.

DABO FM ta tattaro cewa Majalissar ta dakatar da ‘yan Majalissar guda 2 na tsawon watanni 6, bisa cewar tana tuhumar su da wawure wasu kudaden Majalissar.

An dai tashi Dutse- a-hannun-riga a zaman Majalissar na yau Talata

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00