//
Wednesday, April 1

Daliban gidauniyar Kwankwasiyya 105 sun kama hanyarsu ta zuwa birnin Mumbai a Indiya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Dalibai 102 daga cikin 370 da gidauniyar Kwankwasiyya zata dauki nauyin karatunsu don yin Digirinsu na 2 a kasar Indiya, sun kama hanyarsu ta zuwa birnin Mumbai na kasar Indiya.

DABO FM ta tattara cewa; a yau Talata, rukunin daliban 102 suka taso daga jihar Kano bayan kammala taron kaddamar da fara shirin wanda tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Kwankwaso ya jagoranta.

Daliban dai zasu hau Jirgi daga filin tashi da saukar Jirage na Mallam Aminu Kano zuwa filin tashi da saukar Jirage na Murtala Muhammad dake Legas.

Daga nan ne dai daliban zasu hau wani jirgin zuwa birnin Sharjah na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (Dubai) inda daga nan ne zasu tafi zuwa Birnin Mumbai dake kudancin Indiya.

DABO FM ta binciko cewa; Sauran rukunin daliban wadanda zasu sauka a birnin New Delhi, zasu taso daga jihar Kano a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba.

Masu Alaƙa  Katsina: Gidauniyar Kwankwasiyya zata kafa asusun fitar da dalibai karatu kasashen Duniya

Ta bakin tsohon gwamna Kwankwaso, ya bayyana cewa an rarrana tafiyar daliban bisa yanayi na samun kujerar jirgi inda ya bada tabbacin zuwa 2 ga watan Oktobar 2019, dukkanin daliban zasu kammala tafiya.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020