Home LabaraiKano: Hukumar Hisba ta kama ‘Yan Luwad* 50 a wajen casu da suka shirya

Kano: Hukumar Hisba ta kama ‘Yan Luwad* 50 a wajen casu da suka shirya

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Rahotanni daga jihar Kano, Najeriya sun bayyana yacce hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tarwatsa taron ‘shagali’ na murnar zaman tare da wasu da ake zargin ‘yan Luwadi ne, suka shirya.

Rahotan yace hukumar ta fantsama wajen taron chasun yayin da ake shirin fara gudanar dashi a unguwar Sabuwar Gandu ta jihar Kano, suka cafke adadin da ya kai 50, wanda kowanne daga cikin wadanda ake zargi suka gayyato ‘yan uwansu da suke tarayya domin yin murnar kammala karatun wasu daga cikin daga makarantun gaba da Sakandire.

Sai dai bayan da muka tuntubi ofishin hukumar, sun shaida mana cewar ba ‘yan Luwadi bane, sai dai sun tabbatar da cewar ‘yan daudu ne, za kuma suyi mana cikakken bayani da karfe 10 na safe agogon Najeriya da Nijar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00