Labarai

‘Yan sandan Kano sun cafke mutane 100 da suka shiga jihar don fara ta’asar Garkuwa da Mutane

Rudunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke kimanin miyagun mutane 100 tare da muggan makamai wadanda suka shiga jihar domin fara aiwatar da laifin garkuwa da mutane.

Kwamishina yan sandan jihar, CP Ahmad Iliyasu ne ya bayyana haka lokacin da ya tara manema labarai don shaidawa idanuwansu a babbar shedikwatar ‘yan sandan jihar dake Bompai.

DABO FM ta tattaro CP Ahmed yace sun samu rahoton cewa an shirya yin laifukan yin garkuwa da mutane a cikin kwaryar birinin jihar Kano dama garuruwan waje irinsu Wudil da karamar hukumar Garko.

“Mun samu rahotan cewa; an shirya yin garkuwa da mutane a kwaryar Kano, Wudil da Garko da sauran wurare.”

“Wadannan sune suka taho daga garuruwan Bauchi, Kaduna, da kuma dajin Falgore. Sai dai duk munyi nasarar tsayar da aiwatar da sace mutanen da suka shirya dalilin shiri da muke dashi na kawar da barna a jihar Kano.”

CP Iliyasu, a dai dai lokaci da yake nunawa manema labarai makaman da aka kame mutanen tare dasu ya ce;

“Kalli irin makaman da muka kamasu dasu, kalli wannan, banmasan ya sunanta ba. Ko wanda zaiyi farautar Zaki da Giwaye a daji bazai rike wannan mummunar bindigar ba.”

“Sun tabbatar da cewa su masu garkuwa da mutane ne hadi da ‘yan fashi da makami.”

Ya kara da cewa; suna amfani da wadannan kayan (Kayan Sojoji) a wajejen karamar hukumar Tudun Wada da Falgore. Inda ya bada tabbacin tsaurara tsaro a wuraren domin tabbatar da samun zaman lafiya a jihar Kano.

Karin Labarai

Masu Alaka

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun afka kan tawagar Sarkin Pataskum, sun kashe ‘yan tawagarshi 3

Dabo Online

Wasu ‘yan bindiga sun sace wani farin fata, sun kashe 1 a Kano

Ciwon Shawara ya kashe azzalumin mai garkuwa da mutane a Zamfara da Katsina tare da yaranshi 11

Dabo Online

‘Yan Bindiga sun sace surukin babban Dogari ‘ADC’ ga shugaba Buhari

Dabo Online

An fanso dan Majalissar jihar Kaduna awanni kadan bayan anyi garkuwa da shi

Dabo Online

‘Yan Bindiga sun yanka mai unguwa a jihar Sokoto, sun harbe ‘dan sanda 1

Dabo Online
UA-131299779-2