Najeriya

Zauren Maza da Matan Arewa a Instagram ya hada dubu dari 850 don tallafawa Jarumi Moda

A cigaba da tsokaci da binciken shafukan Instagram don ganin irin wainar da mutanen Arewa suke tonawa, yau ma munzo muku da sabon labari mai ban sha’awa.

DABO FM ta binciko shafin Northern Hibiscus Blog, inda muka gano cewa tini dai masu mu’amilla da shafin sukayi hubbasar tara tsabar kudi ta N850,000 a matsayin tallafinsu ga jarumi Moda bisa rashin lafiyarshi da ta kai ga yanke masa kafa.

Wakilin DABO FM a zauren, ya tabbatar mana da cewa tin a makonnin da suka gabata ne shafin ya bada sanarwar asusu don tallafawa jarumin.

A ranar 13 ga watan Yulin 2019, shafin ya bayyana tara N141,000 tare da yin kiran cewa “Muna bukatar kari, ku bada gudunmawa ko da na N500 ne don mu taimakeshi.”

DABO FM ta tabbatar da cewa; a cikin kasa da ‘yan sa’o’i, shafin ya bada sanarwar tara N448,000 daga ma’abota shafin, bayan nan aka ayyana cewa yakamata a tara kudin zuwa Miliyan 1.

A ranar Lahadi, 20 ga watan Yulin 2019, zauren Northern Hibiscus ta bayyana cewa tuni masu mu’amilla da shafin suka tara N834,700, inda mai gudanar da shafin ta bayyana zata cike kudin zuwa N850,000.

Karin Labarai

Masu Alaka

Naman Sallah hakkin Iyayen Samari ne – Martanin ‘Yan mata zuwa ga Samari

Dabo Online

‘Yan Matan Arewa sun bukaci a fara yiwa mazaje gwajin hauka kafin a daure musu aure

Dabo Online

Ina ganin laifin Talakawa, da mutum ya samu kudi sai su yanyameshi – Aisha Falke

Dabo Online

Jarumar barkwanci ‘yar kudancin Najeriya ta yi batanci akan Musulunci

Dabo Online

‘Yan Mata sun fara kokawa kan yadda samari sukayi ƙememe suka hana su kayan Sallah

Dabo Online

‘Yan Matan Arewa sun fara tallar kansu ga Mazan Aure tin bayan Auren yaro ‘dan shekara 17

Dabo Online
UA-131299779-2