Labarai

Yanzu-yanzu: Tireloli dauke da kayayyakin abinci daga Buhari sun taho Kano

Motoci kirar Tirela sama da guda 100 sun kamo hanyar jihar Kano da yammacin yau Talata.

Ma’aikatar kula da ayyukan jinkai da bala’i karkashin jagorancin Haj. Sadiya Umar Faruk ce ta sanar da haka cikin wata sanarwa da ta fitar.

Tirelolin da adadinsu ya kai 110 zasu zo jihar ne domin ragewa mutane radadin dokar zaman gida da gwamnati ta sanya.

Hakan na zuwa ne kasa da awanni 24 da shugaba Buhari ya alkauranta turo tallafi jihar Kano a yayin da ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi a ranar Litinin.

Karin Labarai

Masu Alaka

Babu wadanda suke iya saka katin N100 a tallafin gwamnati – Minista

Dabo Online
UA-131299779-2