Labarai

Sabuwar cuta mai sunan ‘Hantavirus’ ta kara ballewa a kasar China

Sabuwar cuta mai sunan ‘HantaVirus’ ta kara bullowa a kasar China.

Rahotanni daga kasar sun bayyana cewar tini dai aka tabbatar da akalla mutane 32 da suke dauke da cutar kamar yadda sashin Turanci na Global Times dake kasar ta rawaito.

Hakan na zuwa ne bayan da wani da aka tabbatar yana dauke da cutar ya rasa ranshi yayin a kan hanyarshi ta zuwa garin Shandong a ranar Litinin.

Haka zalika sauran mutanen da samu suna dauke da cutar sun shiga mota daya ne tare da mutumin da ya mutu wanda yake dan asalin garin Yunnan na kasar ta Sin.

Masana sun bayyana cewar fitsari da kashin dangogin Bera, Jaba da sauransu ne ke yada cutar.

Ku cigaba da bibiyarmu domin jin mecece ‘HantaVirus’.

Karin Labarai

UA-131299779-2