Yanzu yanzu: Alkaluman ‘Corona Virus’ sun zama 40 bayan sake tabbatar da 4 a daren Litinin

Karatun minti 1

Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 4 da daren yau Litinin.

KAmar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 40.

Da daren yau da misalin karfe 11:00, an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 5. Hukumar tace an sake samun 3 a jihar Legas, 1 a Abuja wanda ya hada jimillar wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 40.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog