0
- A daren Laraba 29 ga watan Afirilu, Allah ya yi wa mahaifiyar Sakataren Kungiyar ‘Yan jaridu na kasa shiyyar Zariya Abubakar Sadiq Muhammed, wato Hajiya Mariya Muhammad rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ta rasu a gidan ta da ke Sabon layi Tudun Wada Zariya, Karamar hukumar Zariya Jihar Kaduna.
Hajiya Mariya, ta rasu tana da shekaru 95 a duniya. Ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama, ciki harda Abubakar Sadiq Muhammed da Musa Muhammed na rundunar ‘Yan sanda ta kasa.
Tuni aka yi janazar ta har da addu’an 7 kamar yadda addinin Islama ya tanadar.
