Labarai

Matakan da karamar hukumar Zariya ta dauka bayan bullar Kwabid-19 – Chairman

Sakamakon taron gaggawa na kwamitin tsaro na karamar hukumar Zariya, Jihar Kaduna ya kira, kwamitin ya dauki matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar sarkewar numfashi ta Covid-19 bayan da aka samu tabbacin bullar cutar karo na farko a karamar hukumar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa daga taron kwamitin, Shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim, wanda mataimakin sa Imam Aliyu Ibrahim ya yi a madadin sa, ya ce, daukar matakin ya zama dole ganin yadda matsalar ke naiman samun mazauni a karamar hukumar.

Bisa matakin da gwamnati Jihar Kaduna ta dauka domin takaita zirga-zirga, a cewar mataimakin shugaban karamar hukumar, ya zama wajibi marawa matakin na gwamnati goyon baya, domin ta haka ne za’a iya gano wanda suke dauke da wannan cuta da ma wanda suka yi mua’amala da mutum na farko da ya kamu da cutar.

Ya kara da cewa, a matsayin su na karamar hukuma, za su dukufa wurin sanya ido a kan al’umma da hana zirga-zirga musamman tsakanin Anguwanni domin kare lafiyar su.

Imam Aliyu, ya nanata bukatar da ake ma al’umma su cigaba da taimakwa manufofin gwamnatin da amfani da shawar-warin masana kiwon lafiya kamar wanke hannu akai-akai da takaita shiga tarukwan Jama’a da amfani da marufin hanci da baki da dai dukkanin matakan kariya.

Daga karshe ya naimi al’umma su yi amfani da lokacin da ake ciki na Azumin watan Ramadana wurin cigaba da addu’oi domin samun sauki akan wannan matsala.

Karin Labarai

Masu Alaka

2020: An samu ruwan sama na farko a Zaria, magudanai sun toshe

Mu’azu A. Albarkawa

Rabon kayan tallafin abincin ya kankama a Zariya, yayin da a Sabon Gari ake shirin farawa – Sani

Mu’azu A. Albarkawa
UA-131299779-2