An kashe Manomi sakamakon rikicin Fulani a jihar Jigawa

An samu mummunan rikici tsakanin Fulani da makiyaya a jihar Jigawa.

Rikicin dai ya faru ne a kauyen Yabaza dake karamar hukumar Birnin-Kudu ta jihar Jigawa.

Rikicin dai daya afku ranar Litinin, wanda yayi sanadiyyar rasuwar Sama’ila Mai Unguwar Yabaza, mai shekaru 80 a duniya

DABO FM ta tabbatar a lokacin rikicin, an hangi Yara da Mata suna gudun tsira dauke da manyan raunuka a jikinsu.

Wakilin mu ya tabbatar mana da ce wa wanda ya rasa rayin na sa Manomi ne, da makiyayan suka afka mana a cikin Daji.

Shugaban kungiyar Miyatti Allah na jihar Jigawa, Alh. Sa’adu Gagarawa, ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Gagarawa yayi Allah wadai da wannan afkuwar lamarin da ya kira ‘neman maido da hannun agogo baya’ akan zaman lafiyar da aka samu a baya.

Masu Alaƙa  Wani Mai gadi ya zabi ayi rijiyar burtsatse a kauyensu da a gina masa gida

Suma a nasu bangaren, rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta hannun kakakinta, DSP Abdul Jinjiri, ya tabbatarwa da DABO FM faruwar al’amarin a dai dai lokacin da wakilinmu ya tattauna dashi a wayar tarho.

Ya kuma bayyana cewa a yanzu haka, rundunar tayi nasarar cafke mutane biyar akan aika-aikar.

Ya bada tabbacin mutuwar daya manomin daya tare da raunatar guda 1 wanda yace a yanzu haka yana kwance a Asibiti.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.