Al'adu

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya mutu

Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe shugaba Robert Mugabe ya Rasu.

Robert Mugabe mai Shekaru 95 a Duniya, shi ne shugaban da yayi fice wajen kawo wa al’ummar kasar ‘yancin kan su.

Ya rasu bayan fama da jinya kamar yadda iyalansa suka fitar da sanarwar.

An dai kifar da Gwamnatin Mugabe a watan Nuwambar shekara ta 2017, wanda ya kawo karshen Mulkinsa da yai zango 3.

An haifi Shugaba Mugabe a ranar 12 ga watan Fabarairu na shekarar 1924.

Yayi zaman Gidan kasu, ba tare da an yanke masa hukunci ba, saboda laifin sukar Gwamnatin kasar a 1964.

A shekarar 1973, a lokacin yana Gidan Yari aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar ZANU, wanda yana daya daga cikin iyayen Jam’iyyar.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yar Gidan Sheikh Ahmad Gumi ta rasu bayan fama da ciwon ‘Amosanin Jini’

Dabo Online

Kungiyar ‘Yan Jaridu ta mika Ta’aziyyar rashin Ma’aikacin NTA

Mu’azu A. Albarkawa

Mahaifin Umar M Shareef ya rasu

Dabo Online

Matashin da yafi kafatanin mutanen duniya gajarta ya mutu a kasar Nepal

Dabo Online

An binne dan Najeriya da ya rasu a kasar Indiya bisa koyarwar addinin Musulunci

Dabo Online

Jigawa: Dan Majalissar Tarayya ya sake rasuwa

Dabo Online
UA-131299779-2