Duniya Labarai

Sama da ‘yan Birtaniya miliyan 1 sun sanya hannu don kada a soke Majalissar kasar

Korafin  yanar gizo-gizo da ‘yan kasar Birtaniya suka shigar na rashin amincewa da bukatar sabon Firaministan kasar na soke majalissar dokokin kasar ya samu goyon bayan mutane sama da miliyan daya.

Dabo FM ta binciko cewa a cikin sa’o’i kadan ne mutanen kasar suka sanya wa korafi hannu rututu.

A shafin da aka wallafa neman sanya hannu ga rashin goyon bayan soke Majalissar, ‘yan kasar sun bayyana cewa “Baza’a soke Majalissar dokokin Birtaniya ba, har sai Kasar ta kara wa’adi ko soke kudurinta na ficewa daga tarayyar Turai.

Bisa yacce kasar ta tsara, ranar 31 ga watan Oktobar 2019 zata fice daga Tarayyar Turai.

Karin Labarai

UA-131299779-2