//

Fadan Kwankwasiyya da Gandujiyya ya fito da ‘Sabon Salo’

0

Siyasar jihar Kano tana cigaba da yin zafi har bayan kammala zaben gwamnan jihar na shekarar 2019.

A dai dai lokacin da tsagin Kwankwasiyya suke ganin sune halastattun wadanda lashe zabe a jihar Kano, gwamnantin jihar ta dauki mataki irin na gallazawa abokan hamayya.

A hali yanzu, a jihar Kano, an shiga wani kangi na kame-kamen abokan hamayya wanda ake danganta hakan da cewa; “Wanda yabi tafiyar Gwamna ya tsira.”

DABO FM ta binciko cewa; daga lokacin zaben gwamnan jihar a watan Maris, an tsare adadin ‘yan tsagin Kwankwasiyya sama da 5.

Idan baku manta ba, a makon daya gabata ne dai aka aike da darakta a Kannywood, Sunusi Oscar, zuwa gidan maza. Kamun da hukumar tace fina-finai take da alhaki.

Masu Alaƙa  ‘Yan sanda sunyi alkawarin kama duk masu hannu a yiwa Pantami ihun ‘Bamayi’

Daga cikinsu akwai mata da mawaka wadanda sukayi irin tasu sukar siyasa a cikin wakensu, wanda suma ba’arsu ba sai da aka tsame.

A wani mawuyacin hali da Najeriya take ciki na karya tsarin doka da oda, rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano, ta nemi mawaki Aminu Ladan (Ala Waka) domin ya amsa tambayoyi.

A lamarin, a iya cewa kiran yana da alaka da wasu wakoki da Ala ya rera a gabannin zaben gwamnan jihar.

Wakoki irinsu “Mai dalli mai Dala, Jan birin uban barna, Baba Uban Abba.”

Duk dai a dambarwar, har yanzu ba’a san a ina matashi Abubakar Idris Dadiyata, yake ba.

Sai dai hukumar DSS ake zargi dayin awon gaba da matashi wanda yayi kauron suna wajen caccaka da adawa da gwamnatin APC a Kano da Najeriya baki daya, tace ba tada hurumin ko hannu game da batan matashin ba.

Karin Labarai

Share.

About Author

•Sublime of Fagge's origin. •PR Specialist •PharmD candidate

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020