Labarai

Yan Sanda sun kwato Daliban Jami’ar ABU 3 daga hannun masu garkuwa da mutane

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta kubutar da Daliban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria guda uku da masu garkuwa da mutane sukayi garkuwa dasu akan Titin Kaduna zuwa Abuja.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Yakubu Sabo ne ya bayyana hakan a yayi da yake shaidawa manema labarai abinda ya faru.

DSP Sabo, ya kara da cewa har yanzu dai akwai ragowar mutane 3 da akayi garkuwa dasu, wadanda aka daukesu tare da daliban.

“Ranar 26 ga watan Agusta da misalin karfe 6:50 yamma, wasu mutane sanye da kayan Sojoji dauke da muggan makamai sun tare wa matafiya hanya hade da harbi Bindiga a dai dai wani kauye da ake kira Masari a hanyar Kaduna zuwa Abuja wanda shine yayi sanadiyyar sace mutane shida.”

“Kawo agajin gaggawa daga ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro ne yayi sanadiyyar ceto mutane 3 daga cikin wadanda masu garkuwar suka dauke bisa dalilin matakin da jami’an suka dauka.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya rawaito cewa; Rundunar ‘yan sandan tace “Sun tafi da Daliban guda 3 tare da motocin da aka bari bayan lamarin ya faru zuwa ofishin ‘yan sanda.

Runudunar ta tabbatarwa manema labarai cewa shirye shirye yayi nisa domin ganin an kubutar da ragowa mutanen daga hannun masu garkuwar tare da tabbatar da cewa masu laifin sun shigo hannu domin su girbi abinda suka shuka.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yan Sanda sun samu nasarar bundige Iblis a Najeriya

Na sace kanwata na nemi kudin fansa miliyan 10 don zuwa kasar waje karatu -Matashi

Muhammad Isma’il Makama

#JusticeForKanoKids: ‘Yan sanda sun sake kubutar da Yaran Kano 2 daga Anambra

Muhammad Isma’il Makama

Wani malami a babbar makaranta dake kano ya amsa laifin haike wa dalibarsa

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan Shi’a sun kashe DCP Umar Usman tare da cinnawa motocin ‘NEMA’ wuta

Dabo Online

‘Yan sanda sunyi alkawarin kama duk masu hannu a yiwa Pantami ihun ‘Bamayi’

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2