Sambo Dasuki yana nan a raye – Hukumar DSS

Karatun minti 1

A ‘yan kwanakin nan tin bayan kammala zaben shugaban kasa da ‘yan majalissar dattitai da wakilan, labarai suke ta yawo a kafafen sada zumunta na cewa Sambo Dasuki ya rasu.

Sai dai hukumar DSS ta Najeriya ta karyata wannan batu kuma ta bada tabbacin yana nan da ransa cikin koshin lafiya.

Kotuna da dawa na cikin Najeriya dama kungiyar ECOWAS sun umarci gwamnatin Najeriya da ta bada belin Dasuki, sai dai gwamnatin Najeriya tayi kunnen kashi bisa umarnin kotunan, inda tace tana cigaba da tsareshi saboda tana daukaka kara.

Suma a nasu bangaren, ‘yan jarida sun nemi damar shiga inda Dasuki yake a tsare domin su ganewa idonsu inda har ya bada damar a daukeshi a hoto domin a nunawa duniya cewa yana nan da ranshi.

Gwamnatin Najeriya dai na zargin Dasuki, wanda yake tsohon mataimakin shugaba Goodluck Jonathan akan harkokin tsaro, bisa yin sama da fadi tare da rabar da kudin da gwamnatin Jonathan ta ware domin fada da masu tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog