Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kotu ta cire sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jami’iyyar PDP

1 min read

Wata Kotu mai zaman kanta a jihar Kano ta ruguje Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jami’iyyar PDP.

Mai shari’a Justice Lowis Allagoa ya baiwa jami’iyyar PDP reshen jihar Kano damar sake zaben fidda gwani kafin ranar Asabar da za’a gudanar da babban zaben gwamnoni.

Sai dai a nata bangaren, jami’iyyar ta hannun shugaban riko na jami’iyyar ta PDP reshen jihar Kano, Engr Rabi’u Suleiman Bichi yace hukuncin kotu bai shafi dan takarar gwamnan Abba Kabir Yusuf ba.

Bichi yace rikici ne kawai na jami’iyyar kuma dan takararsu zai cigaba da yakin neman zaben da yakeyi.

Tini dai jami’iyyar ta PDP ta daukaka kara.

 

Sauran labari na zuwa

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.