(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Wallahi munyi aringizon ƙiri’u a Kano, – Wani Jagoran APC a Kano

Karatun minti 1

Wani faifan murya daya dauki hankalin al’umma musamman yan jami’iyyar PDP a jihar Kano, faifan muryar da ake zargin muryar wani jigo ne a jami’iyyar APC dayin waya tare da wani abokinshi dake jihar Jigawa.

Jigon na APC mai suna Kamilu ya baiwa abokin nashi labarin yadda sukayi aringizon kuri’a a zaben da aka gudanar na shugaban kasa tare da ‘yan majalissar dattijai hadi dana wakilai.

Hon Kamilu ya bayyanawa abokin nashi cewa jami’iyyar APC ta fadi wasu kananan hukumomi a cikin Kano.

“Doguwa, Tudun Wada, Kumbotso, Kunci, Shanono, Bagwai, Dawakin Tofa, duk aringizo mukayi wallahi.”

“An rike sakamakon karamar Hukumar Nassarawa, Tarauni, Dala da karamar hukumar Birni saboda munso mu baiwa Buhari kuri’a miliyan 2.”

“Wallahi tallahi an karawa Shekarau kuri’a dubu dari biyu.”

SAURARI FAIFAN MURYAR

SAURARI FAIFAN MURYAR

Karin Labarai

Sabbi daga Blog