Sarki Sunusi ya koma Kano bayan da aka sasantashi da Ganduje a Abuja

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, ya koma jihar Kano jim kadan bayan gama sasantashi da gwamnan jihar Dr Abdullahi Ganduje.

Tin a jiya juma’a ne bayan an gudanar da taron gwamnonin Najeriya wanda shugabansu na jihar Ekiti, Fayemi ya jagoranta, an kawo karshen dambarwar dake tsakanij gwamnan da kuma Sarki, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

Dambarwar ta faro asaline tin shekarar 2016-17, yayin da ta kara tsamari dai dai lokacin da aka gudanar da zaben gwamna a jihar Kano.

Gwamnatin Ganduje dai ta zargi Sunusi da goyon bayan dan takarar gwamnan a PDP, Abba Kabir Yusuf.

Kalli bidiyon dawowar Sarkin
Masu Alaƙa  Kowanne 'dan Najeriya yana da cikakken 'yanci a duk jihar da yake zama - Sarki Sunusi

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.