Labarai

Sarkin Kano Sunusi ya zama shugaban Jami’ar gwamnatin jihar Borno

An Sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sunusi II, a matsayin shugaban jami’ar gwamnatin jihar Borno.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Umar Kyari Sandade tare da babban sakataren ma’aikatar Ilimi ta jihar Borno tare da wasu masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a jihar ne suka mikawa mai martaba Sarkin Kano takardar shaidar zamanshi shugaban jami’ar.

SOLACE BASE ta rawaito an baiwa sarkin takardar a ranar Asabar a fadarshi dake gidan Dabo.

Farfesa Umari Kyari ya shaidawa mai martaba cewa an nada shi shugaban makarantar ne bisa kwazo da kwarancewa.

Da yake karbar nadin, Mai martaba Muhammadu Sunusi II ya bayyana jin dadinshi tare da bada tabbacin yin amfani da kwarewarshi wajen ciyar da jami’ar gaba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sarki Sunusi ya tsige limami a Kano bayan ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi akan ganin wata

Dabo Online

An shawo kan rashin jituwar Ganduje da Sarki Kano Sunusi

Dabo Online

Malamai miliyan 1 na kasar Kanada sun nada Sarkin Kano shugaban kwamitin ‘Mashawarta’

Dabo Online

Sarkin Kano Sunusi II ya zama shugaban jami’ar gwamnatin jihar Ekiti

Dabo Online

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Buhari bai shiga maganar sasanta Ganduje da Sarkin Kano ba – NTA

Dabo Online
UA-131299779-2