Labarai

Satar yara a Kano: Fiya da yara 38 yan kasa da shekaru 3 aka sace a karamar hukumar Nassarawa

A wani bincike da Dabo FM tayi ta gano an sace yara 38 a cikin wata 8 kacal a karamar hukumar Nassarawa dake birnin Kano, bayaga alhinin da aka shiga na sace yara 9 yan asalin jihar tare da chanza musu addini zuwa kiristanci.

Rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da faruwar hakan bayan binciken sirri da jaridar tayi a labarin da ta wallafa na sace yara 9 tare da siyar dasu a jihar Anambra.

Tin shekarar 2014 ake ta wayar gari kusan kullum ana dauki dai-dai na kananun yara da basu wuce shekaru 3 ba musamman a unguwannin Hotoro, Hotoron Arewa, Hayi, Tinshama, Wurabaggo da dai sauran unguwanni duk cikin karamar hukumar Nassarawan kuma har yanzu babu labarin su.

‘Yan Sanda na iyakar kokarin su saidai kuma mutane na ganin yawan cin gidajen jaridu da sauran mutane sunyi kurum musamman ma bisa abubuwa da suka faru shekaru kadan da suka wuce akan wata yarinya mai suna Eze.

Tini kiraye kiraye sunyi nisa a gidajen rediyo da shafukan sada zumunta na ganin an tabbatar da adalci.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ganduje, Sarki Sunusi sun jagorancin daurin auren Zaurawa 70

Dabo Online

Covid-19: Ganduje ya sanya dokar hana shiga ko fita daga Kano ta kowacce hanya

Dabo Online

Katsina: Gidauniyar Kwankwasiyya zata kafa asusun fitar da dalibai karatu kasashen Duniya

Muhammad Isma’il Makama

Akwai yiwuwar dasa abubuwan fashewa a guraren zabe, kasuwanni da guraren bauta – Masu Sa’idon Zabe

Dabo Online

Da alama jami’an kula da ‘Gidan Zoo’ a Kano sun tsare kudin da aka tara da Babbar Sallah daga Goggon Biri

Dabo Online

‘Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

Dabo Online
UA-131299779-2