//
Tuesday, April 7

#JusticeForKano9: Ganduje ya yaba wa Jami’an tsaro, yayi kira ga Iyaye su kula sosai

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya jinjina wa rundunar ‘yan sandan jihar Kano, bisa kokarinsu na ceto Yaran nan guda 8 da aka samo a jihar Anambra.

Tin a karshen makon nan ne, hukumar ‘yan sanda ta kwato wasu Yara guda 9 wadanda tabi kadin sace su har zuwa garin Onitsha na jihar Anambra inda Jaridar Daily Nigerian ta tabbatar da an sauyawa yaran addini zuwa Kiristanci a jihar.

Gwamna Ganduje, ya yabawa jami’an tsaro tare da jinjina musu bisa jajircewarsu wajen ceto Yaran.

“Iya wannan namijin kokarin, ya isa abin kwarai, hakan ya nuna zahirantuwar jajurcewar Jami’an tsaron Najeriya ta fuskan tabbatar da kawar da miyagun ayyuka.”

Masu Alaƙa  Kotu ta cire sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jami'iyyar PDP

Gwamna ya alakanta kokarin rundunar ‘yan sandan jihar Kano da yin amfani da kayayyakin zamani wajen zakulo masu laifi a wuraren buyarsu na jihar Kano.

Gwamnan ya kuma yi alkawari cigaba da baiwa rundunar gudunmawa ta hanyar cigaba da sama musu kayayyakin zamani.

“Da taimakon Allah, jami’an tsaronmu suna yin aiki tukuru ba dare ba rana, wanda jihar Kano tana moruwa daga wannan kokarin.”

“A yanzu Kano, ta zama ba wajen zaman masu aikata miyagun laifuffuka ba.”

Daga karshe, gwamnan yayi kira ga iyayen Yara da su zama masu sa ido akan ‘yayansu.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020