A wani mataki na ban mamaki bayan kammala sauraren muhawarar lauyoyin APC, PDP da INEC, Shari’ar zaben gwamnan tana neman sauya zani.
Duba da irin kwarin gwiwa da a iya cewa ‘ya yan jami’iyyar PDP a Kano suke dashi na cin nasara a Shari’ar Gwamnan.
Da yake bayani, lauyan INEC, Ahmad Raji SAN, ya ce an baiwa Jami’iyyar PDP damar bayyana sahihan takardun shaida a kotu amma yawancin takardun shaidun ba sahihai bane, saboda haka, ya bukaci kotu tayi watsi da karar. –Legit Hausa ta tabbatar
Shima a nashi bangaren, lauyan dake kare Gwamna Ganduje, Offiong (SAN), ya ce jam’iyyar PDP ta gaza gabatar da sakamakon da ta tattara da kanta amma ta dogara kan sakamakon da hukumar INEC ta sanar, saboda haka, kotu tayi watsi da karar.
Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa; “Lauyan APC, Alex Izinyon SAN, ya ce jam’iyyar PDP da Abba Kabir sun yi zargin cewa an saba doka wajen soke sakamakon zaben akwatunan zabe 207 amma basu gabatar da hujjoji akai ba. Saboda haka, kotu tayi watsi da karar.”
Sai da a nasu bangaren lauyoyin PDP ta hannun Kanu Agabi SAN, ya ce babbar hujjarsu itace Abba Kabir ne ya lashe zaben zagayen farko a ranar 9 ga Maris 2019. -Legit Hausa.
