//
Wednesday, April 1

N21,150 ne kudin makarantar ‘Capital School Kaduna’ – Principal

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban makarantar Capital School dake jihar Kaduna, Mallam Ibrahim Yunusa, ya bayyana cewa; N7,050 ne kudin makarantar a kowanne zangon karatu.

Biyo bayan shigar dan gidan gwamna El-Rufa’i, makarantar Capital School ta jihar Kaduna, al’umma da dama suke ta magantuwa akan lamarin.

Wasu na yabawa gwamnan bisa yunkurin da yayi wajen ceto Ilimi a jihar, inda a daya bangaren wasu ke ganin ba abinda za’a yaba bane domin makarantar asalinta ta masu kudi ce.

Hakan yasa DABO FM ta tattaro daga wata zantawa da sashin Hausa na BBC yayi da shugaban makarantar, Mallam Ibrahim Yunusa.

Malamin ya bayyana cewa, ita dai makarantar Capital School, ba makaranta ce ba kamar sauran makarantun jihar ba, domin makaranta ce da aka kafa ta domin ‘ya ‘yan manyan ma’aikatan gwamnati.

Masu Alaƙa  Yanzunan: 'Yan bindiga sun harbe mutum 66 a Kaduna

“Bambancin babu yawa, lokacin Sardauna aka gina Capital School, saboda ‘ya ‘yan manya suyi karatu a ciki.”

Ya kuma bayyana cewa ana biyawa kowanne yaro N7,050 a kowanne zangon karatu daga cikin zango 3 da ake dashi.

A kowacce shekara, ana biyawa kowanne dalibi dake bangaren Firamare, N21,150.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020