0
Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari rasuwa a yau Juma’a. Ya rasu a wani babban asibitin dake birni Abuja a Najeriya bayan fama da wata gajeriyar rashin lafiya.
Rahotan rasuwar ya fito daga wajen jikansa Bello shagari wanda ya wallafa a shafinsa na twitter.
Shehu Shagari rasu yanada shekaru 93.
Takaitaccen tarihi:
Ranar Haihuwa: 25th February 1925
Gari: Sokoto
Shehu Shagari shi ne shugaban Najeriya na farko kuma na karshe a jamhuriya ta biyu a Najeriya.
Allah ya jikansa ya kuma yi masa rahama.
