/

An amince da hukuncin kisa a kan masu cin zarafin kananan yara a Indiya

Karatun minti 1

Gwamanatin kasar Indiya ta amince da dokar kisa a kan masu cin zarafin kananan yara a karkashin dokar “Protection of Children from Sexual Offences”

Rahotan daga kamfanin dillaninci labarai na ANI a kasar ta bayyana cewa ministan shari’a kasar Mr Ravi Shankar Prasad ya bayyana hakan ne bayan amincewar bangaren zartarwa na kasar.

Al’ummar kasar da yawa sun bayyana jin dadinsu ga wannan doka wacce suka dade suna fatan samun irinta.

An   tabbatar da dokar ne a yau Juma’a, 28 ga Disambar 2018.

Kasar India dai tayi shura wajen samu matsaltsalu fyaden kananun yara, sai dai itama gwamnatin kasar ba ta gazawa  wajen hukunta duk wanda aka kama da laifin.

Shin ya dace kasar Najeriya tayi irin wannan dokar? Zaku iya bayyana ra’ayinku a shafin na Facebook, Twitter da Instagram.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog