Labarai

Sheikh Zakzaky yana kan hanyarshi ta dawowa Najeriya daga kasar Indiya

Shugaban kungiyar IMN, Mallam Ibrahim Zakzaky yana kan hanyarshi ta dawowa Najeriya daga kasar Indiya.

Muna hada wannan rahoto ne da misalin karfe 11:00 na daren Indiya, wanda haka ya tabbattar da cewa Sheikh Zakzaky ya shafe awa guda a sararin samaniya.

Shafin dake yada lamuran Malamin ne ya bayyana haka a shafinsu na Twitter.

Tin dai a ranar Talata, Dabo FM ta samu rahoto daga wakilanmu na kasar Indiya cewa; Malamin ya kammala shiryawa domin dawowa Najeriya biyo bayan takadamma taka auku tsakanin Malamin da wasu hukumomin Gwamnati.

Mun rawaici cewa; Yan Shi ar kasar Indiya sun shirya zanga-zanga domin kubutar da Mallam Zakzaky daga abinda suka kira “Kurkuku.”

Hakan ya saka gwamnatin kasar Indiya ta kalli matakin nasu a matsayin wani shiri na yiwa zaman lafiyar kasarta barazana.

Kasar Indiya bata lamuntar babbar zanga-zanga, domin da zarar an fara zanga-zanga waje, gwamnatin take gintse “Intanet” domin hana fitar bayanai.

Sharadin da gwamnatin Indiya ta bawa Zakzaky na cewa “Ko ya amince, ko ya bar mata kasa” yafi alakantuwa da yunkurin yin zanga-zangar da mabiya Shia a kasar suka shirya. – Kamar yacce majiyoyinmu suka tabbatar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Shugaban tsohuwar kungiyar IMN ta Shi’a, Mal. Ibrahimul Zakzaky zai tafi kasar Indiya a yau

Dabo Online

Kotu ta bayar da belin Al-Zakzaky don neman lafiya

Dabo Online

Shugaban ‘Haramtacciyar’ kungiyar IMN ta Shi’a, Mal. Ibrahimul Zakzaky ya tashi zuwa kasar Indiya

Dabo Online

Duban Lafiyar Sheikh: Kasar Iran ta yabawa shugaba Buhari kan El-Zakzaky

Dabo Online

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin bayyana kungiyar Al-Zakzaky a matsayin ‘Kungiyar Ta’addanci’

Dabo Online

Ku bamu Al-Zakzaky zamu kula da lafiyarshi – Iran ta fadawa Najeriya

Dabo Online
UA-131299779-2