Nishadi

#SunusiOscar442: Adam A. Zango ya fice daga Masana’antar Kannywood

Fitaccen jarumi Adam A. Zango ya ce ya fice daga masanaantar fina-finan Hausa ta Kannywood.

Zango ya bayyana ficewar tashi daga Kannywood a shafinshi na Instagram a ranar Alhamis, 15 ga watan Agustar 2019.

DABO FM ta rawaito Adamu Zango yace; “Daga yau 15 ga watan August, ni Adam A. Zango na fita daga kungiyar shirya fina-finai ta Kannywood.”

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kama mai bada umarni a masana’antar, Sunusi Oscar, wanda ake alakanta kamun nashi da bambancin ra’ayin siyasa.

Adam Zango ya tabbatar da ficewarshi tare da bada sanarwar cewa daga yanzu dukkanin abinda ya aikata ko kuma ya shafe shi, bashi da alaka da masana antar Kannywood.

“Daga yau duk abinda na aikata mai kyau ko marar kyau, kada a dangantashi da Kannywood.”

Ya kara da cewa; “Wannan hakki na ne, kada al’umma suyi min mummunar fahimta. Babu dokar kungiyoyinta a kaina.”

Sai dai Adam Zango ya ce ya fita daga masana’antar ne bisa dalilin shugabancin ka ma karya da akeyi a masana’antar ne ya saka ya fita.

Daga karshe ya kuma yi kira ga ‘yan wasa a masana’antar da duk mai son yin aiki da shi, ya biyo shi a inda yayiwa kanshi lakabi da “Jarumi mai cin gashin kanshi.”

View this post on Instagram

BA LAIFI BANE GA DUK WANDA YACE FITA DAGA KANNYWOOD. . MISALI….. INDIA SUNA DA_BOLLYWOO SUNA DA SUNA DA MOLLYWOOD SUNA DA TOLLYWOOD. . DAGA YAU DUK WANDA ZAIYI AIKI DA NI. A SHIRYE NAKE AMMA BANDA KANO DON GUDUN KADA IN KARYA DOKAR YAN KANNYWOOD. #independentfilmmaker . @realalinuhu @realsanidanja @official_hafsaidris20 @ayshatulhumairah @asmuhammed @official_sarat2 and Others @kadunafilmacademy1 @yusufbellodankundalo @kaulahabina @hassan_giggs @tyshaban @garzalimiko @yunusamuazu1 @sk_custumes @rikadawa1 @real_cousin @nurahudu40 @sani_candy @naseer_naba7 @salisufulani10 @official_sanaco @babawowushishi30 @aleegumzak @alhajisheshe @danhajiyafilms @danjumafkd @tahiritahir_abba @real_iznaku @kannywoodscene @real_kb_international1 @zahraddeen_karmatako @falalu_a_dorayi @real_nfeenah @offical_faezah @washafati @yakubmohammed_ @teemanmamanta @elmuaz @kannywoodcelebrities @queen_bachure @kannywoodexclusive @kb2effects @ijey_fyne @balancy_photogallery @xaqi616 @adam_a_zango @xclusive_people @hamza_dogo_dandago @abdulamart_mai_kwashewa @abba.soso.121 – #regrann – #regrann – #regrann

A post shared by GOD MADE KING🇳🇬👑🇳🇬 (@adam_a_zango) on

Masu Alaka

KANNYWOOD: Ban tsugunna har kasa don bawa Nabruska hakuri ba – Hadiza Gabon

Dabo Online

Maryam Booth za ta raba buhuhunan Shinkafa, Mai da sauran kayayyakin abinci

Dabo Online

Zamani Riga: Me duniyar Kannywood take ciki a Yau da nasarorinta?

Dabo Online

Ali Jita ya raba wa ‘Almajirai’ rigunan sanyi da barguna

Dabo Online

Nafison fitowa a matsayin fitsararriya a wasan kwaikwayo – Maryam Yahaya

Dabo Online

Kotun ta bawa CP Wakili umarnin kama Hadiza Gabon

Dabo Online
UA-131299779-2