Umar Aliyu Fagge
Ra'ayoyi

Shigar Malamai Siyasa ba matsala bane, daukar bangare ne matsala, Daga Umar Aliyu

MECECE SIYASA?

Siyasa tana nufin kyakyawar mu’ammila tsakanin mutum da sauran alummar ususan mutumin da yake jan ragamar alumma ta fuskar shugabanci ko wakilci, mutum yana iya zama mai kyakyawar mu’ammila ne sakamakon ilimi ko wayewa da sanin abubbuwan dake cikin wannan duniyar tamu yar yayi.
Kyakyawan shugabanci shi ne wanda aka dorashi bisa doron ilimi, ba son rai ko rashin sani ba.
Idan muka yi la’akari da wannan ma’anar ta shugabanci zamu fahimci cewa kuskure ne wasu daga cikin mutane sun ringa tunanin cewa wai malamai bai kamata su shiga siyasa ba, idan har malamai basu shiga siyasa ba suwa muke tunanin su ja ragamar alumma cikin samun nasara ta fuskoki daban-daban?
A maimakon mu kore malamai daga cikin siyasa kamata yayi muyi amfani da ilimin su gurin samun tsabtattacen shugabanci, mu da ake mulka ne ya kamata mu zubawa malamai ido gurin ganin sunyi amfani da damar da Allah ya basu gurin hakaitar da shuwagabanni ko tsawatar musu akan abin da ya sabawa koyar wa addinin musulunci.
Shigar malamai siyasa ba matsala ba ne, daukar bangare ne matsala.
Malamai kamata yayi su zama bulaliya tsakanin malam talaka da shugaba gurin nunawa shuwagabanni abin da ya dace su aiwatar wa alummar da suke wakilta kuma dukkan bangare biyun (shugaba da alummar da ake mulka) masu biyayya ne ga umarni ko shawarwarin malamai domin sun cancanta a saurare su ba wai su saurari umarnin wani ba.
A duk lokacin da malamai suka tsare mutuncin su tare da gudun abin hannun jami’an Gwamnati tabbas alumma zasu samu ingataccen shugabanci tare da tsawatar wa shuwagabanni a duk inda suka sauka daga kan layi, malamai alkalai ne ba masu bawa wani kariya ba.
Da zarar malamai suka shiga siyasa ba da zummar kawo gyara ba face goyon bayan Gwamnati, to hakan dai-dai yake da sun siyar da daraja da kimar da Allah ya basu a matsayin magada Annabawa a ban kasa, a maimakon kowane mutum ya saurari umarni ko shawarar su sai a koma nuna musu yatsa da danganta su da Gwamnatin da suke goyon baya wanda hakan ba karamin nakasu yake kawowa addini ba.
Ya zama lallai malamai su yarda su iyayen kowa ne ta hanyar yin amfani da damar da Allah ya basu gurin isar da sakon shi izuwa sauran mutane ta hanyar da ya dace ba wai su ringa yin amfani da wannan damar ba gurin neman abin duniya a gurin wasu gama-garin shuwagabanni.
Abubuwan da suka faru a jihar kano kwanan nan ba komai ba ne illa barin tafarkin koyarwar addinin musulunci da wasu daga cikin malamai masu neman abin duniya suka yi, wanda inda ace malamai sun tsaya akan aikin su da ba a samu yawaitar fusatattun matasa marasa tarbiya sun haikewa daya daga cikin malamin addini wanda bai kamata ayi masa hakan ba.
Afkuwar hakan ke da wuya wasu daga cikin fusatattun malamai suka yi amfani da wannan damar gurin bayyana fushin su ga wani bangare da suke takun saka da shi a siyasance, wanda hakan ya bude shafin cece-ku-ce a tsakanin wanda abin ya shafa.
Dole fusatattun malamai su tsayar da kafafun su a matsayin iyaye ga kowa ba tare da daukar wani bangare ba na siyasa, su kuma fusatattun yan siyasa su mutunta tare da bawa malamai girman su don ganin abubbuwa sun tafi yadda ya kamata ace sun kasance.
Rattabawa
Umar Aliyu Fagge
05/10/2019

Masu Alaka

‘Yar Najeriya mai shekaru 21 tayi fice bayan kammala karatun kiwon lafiya a kasar Turkiyya

Dabo Online

Rigar ‘Yanci: Dama nasan za’a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin ‘yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

Dabo Online

Zuwa ga masu neman a baiwa Mata limancin Sallah da nufin ‘Kare hakkin Mata’ daga Bin Ladan Mailittafi

Dabo Online

Taskar Matasa: Ga wanda suke tunani mai kyau, Daga Umar Aliyu Fagge

Zamu zama tsani tsakanin masu mulki da wandanda ake mulka – Majalisar Matasan Najeriya

Mu’azu A. Albarkawa

Kwanaki 217 da bacewar Abubakar Idris Dadiyata

Dabo Online
UA-131299779-2