Labarai

Kano: Ina so a kaini gaba domin a gyaramin kuskure na – Mai Shari’a Halima Shamaki

Mai Shari’a Halima Muhammad Shamaki, ta bayyana cewa tana bukatar duk wanda bai yadda da hukuncin ta da ya daukaka kara.

Dabo FM ta tattaro cewa mai shari’ar ta bayyana haka ne yayin gudanar da Shari’a tsakanin gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje da dan takarar PDP, Abba Yusuf.

“Ku sani mu ‘yan Adam ne, kamar yacce muka fada tin farko, bamu wuce muyi kuskure ba.”

“Ina kiran mutanen Kano su zauna lafiya, Kano gari na ne na biyu, idan aka tayarda hankalin bazamu ji dadi ba.”

Halima Shamaki, ta kara da cewa zasu samu sakamakon zama a jihar idan har ‘yan jihar sun bi doka kuma suka zauna lafiya.

“Mun shafe tsawon watanni 6 muna wannan Shari’a, za’a biya mu zaman da mukayi a jihar ne kadai idan aka zauna lafiya.”

“Zamuyi matukar farin ciki cewa hanyar daukaka kara don gyara mana kuskure itace kadai wanda hukunci bai yiwa dadi ba zai dauka.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kai Tsaye: Daga Kotun sauraren karar zaben shugaban Kasa

Rilwanu A. Shehu

Kotu ta kori karar Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da Ganduje

Dangalan Muhammad Aliyu

Har yanzu ina cikin dimuwar saukalen da kotin koli tayi min -Tsohon Gwamnan Imo

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje na cikin jerin gwamnonin dake fuskantar barazanar tsigewa daga kotun ƙare kukan ka

Muhammad Isma’il Makama

Kano: Kotun daukaka kara ta tabbatar wa Hon Shamsuddeen Dambazau na APC kujerarsa

Muhammad Isma’il Makama

Kotun Koli ta karbe kujerar gwamna daga PDP ta bawa APC mai mulki

Dabo Online
UA-131299779-2