Muhammadu Buhari

2023: Zuwa yanzu bani da niyyar ‘kara tsayawa takara a karo na uku -Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne domin kawo karshen kunji-kunjin da yake yawo a shafukan sada zumunta cewa wai yana shirin canja kundin tsarin mulkin Najeriya domin samun damar sake tsayawa takara a 2023.

Dabo FM ta jiyo mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, yana cewa: ” Shugaba Buhari zai kammala wa’adin sa na biyu sannan ya tattara nasa-ina-sa ya fice daga gidan gwamnati. Za a yi zabe a wannan lokaci kuma ba zai kara tsayawa takara ba kamar yadda tsarin mulki ya tanada.”

Kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar, Shehu ya ci gaba da cewa babu wannan magana kuma ma dai Buhari ba irin wadancan tsoffin shugabannin bane.

Masu Alaƙa  Buhari zai kai ziyarar sirri zuwa kasar Birtaniya a yau Alhamis

” Buhari mai bin doka ne sau da kafa, ba zai taba yin wani abu da zai kawo rudani a kasa ba. Idan wa’adin mulkinsa ya cika, zai tafi.”

“Idan ma wani ya nemi yin wani abu kamar haka, ba zai samu goyon bayan shugaban Buhari ba.”

“A da an samu labarin wasu sun so su yi haka amma abin bai yiwu ba. Buhari ba zai taba yin abin da ba haka yake a doka ba.”

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.