Shugabanci ne matsalar Najeriya da Arewa, Daga Umar Aliyu Fagge

Kalmar shugabanci kalma ce da take nuni da wani babban matsayi da mutum yake da shi ko ya rike a cikin al’umma, wannan matsayin ba kowane mutum bane ya dace da shi face akilin mutum ma’abocin hankali wanda ya kudirci niyar hidimtawa alumma ta hanyar sadaukar da lokacin da gurin kare musu dukiyoyi, rayuka da mutuncin su.

A kasashen da suka cigaba kuma suka san abin da sukeyi, mutum baya zama shugaba koda na kwasar kashi ne, ba tare da yana da wata manufa ko tsarin da zai ciyar da wannan al’umma gaba ba.

A kullum shugabanci a gurin mutanen da suka san abin da sukeyi, wata dama ce da zaka hidimtawa kasarka ta hanyar sadaukar da lokaci da tunanin ka ta yanda ko bayan ka gushe al’umma zasu rinka tuno alherin da ka assasa a lokacin da suka damka maka amanar su ta tsawon zango ko wa’adin mulkin ka.

Masu Alaƙa  Su Waye ke bautar da Matasa a manhajar Facebook?

A gurin su ba damar da zaka ha’inci al’umma ba ne ta hanyar dibar arzikin kasa gurin azurta kanka da iyalan ka, hanya ce ta hidimtawa kasa da yan kasar baki daya ta yadda kowa zai ringa alfahari da salon shugabancin ka ba tare da la’akari da bambamcin jam’iya ko addini ba.

Amma idan  muka waiwayo nan gida Najeriya abin yasha bambam da sauran kasashen da suke da jajajirtattu kuma adalan shuwagabanni, domin mu a nan gida Najeriya mutane basu san meye shugabanci ba ballanatana su san nauye-nauyen da ya rataya a kan shi shugabancin.

Kullum burin mutum ya za’ayi ya zama shugaba a kowane matakin rayuwa ya tsinci kan sa, duk tunanin mu a guri daya yake ta yawo ba kamar sauran mutanen kasashen da suka fahimci rayuwa ba.

Masu Alaƙa  Ko mutanen Arewa zasu so Kwankwaso irin soyayyar da Buhari ya samu?

Tun daga matakin kungiyoyi har izuwa karamar hukuma, jiha da kasa baki daya bamu da wani buri face ace wanin mu ya zama shugaba, ba tare da ya kawo wani ingantaccen tsarin da zai amfanawa al’ummar da ya jagora ba.

Tunanin shuwagabanninmu bashi da wani inganci da har wanda  da ake mulka zai yi alfahari dashi, a maimakon kaga shuwagannin mu na bude makarantu da kamfanoni domin cigaban alummar da ake mulka sai da kaga sun buge da rabawa matasa masu yi musu tumasanci da maula kudi a kafafen sada zumunta. Wanda hakan yana yi wa yan baya nuni da su riki tumasanci a matsayin aikin yi tunda har shuwagabanni suna iya kyautatawa masu yin hakan!

A kasashen da suka san me shugabanci yake nufi kullum kokarin su ta yaya zasu kirkiri wata hanya da zata hana matasa da alummar wannan kasar aikin tumasanci da nadama, domin sun yarda cewa amana aka basu kuma duk wanda ya gaja kare hakkin alumma kamar ya cutar dasu ne.

Masu Alaƙa  ‘Yan siyasa na amfani da kalmar “Hassada” ko “Bakin ciki” don dakushe masu musu hamayya

Shi yasa kullum ba zaka ji ko kaga sauran shuwagabannin kasashe suna karfafa aikin jagaliyanci da tumasanci ba, domin abu ne da yake lalata rayuwar matasa idan matasa suka gurbata tamkar kasa ce ta gurbata.

Wannan kadan daga cikin tunanin masu son zama shuwagabanni ne a jiha ta kuma nahiya ta, yake nuna bajintar sa da irin tunanin sa dangane da alummar da yake son shugabanta.

⬇⬇⬇
Rattabawa

Umar Aliyu Musa Oumaraliyu@gmail.com

21/9/19

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.