(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Siyasa: Mallam Aminu Kano ya fara siyasa yana ‘dan shekara 23

dakikun karantawa

Mallam Aminu Kano ya fara siyasa lokacin da yake samartaka da kuruciya.

Ya fara siyasa yana dan shekara 23 da haihuwa.

An dai haifi Mallam Aminu Kano a shekarar 1920, shekaru 40 kafin karbar ‘yancin Najeriya.

Ya rasu yanada shekara 63 a duniya, tarihi ya nuna Mallam Aminu Kano ya shafe shekaru 40 yana gwagwarmayar siyasa domin nemawa talaka ‘yanci da sauke masu mulkin kama karya a Najeriya.

Malam aminu kano yafara tunkarar harkokin siyasa ne tun a shekarar 1943 lokacin daya taimakawa Malam Sa’adu Zungur wajen kafa kungiyar “Cigaban Bauchi a jihar Bauchi” a shekarar 1946.

Mallam Aminu Kano da Mallam Sa’adu Zungur sune suka karfafa kafuwar jam’iyar NEPA wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE ASSOCIATION kafin daga baya takoma NEPU (NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE UNION).

Ankafa jami”yiyar ne a 8 ga watan Agusta na shekarar 1950, wanda aka fara kafa ta da mutane 8.

A shekarar 1947 ne Mallam Aminu Kano ya jagoranci bude wata kungiya ta malaman arewacin Najeriyar, kuma dashi aka bude jam’iyyar mutanen arewa wadda daga baya takoma LPC a shekarar 1949, sababin jami’iyyar shine don taimakawa mutanen Arewa.

Malam Aminu kano ya rungumi harkokin siyasa sosai wanda har hakan tasa ya ajiye aikinsa a ranar 4 ga watan Nuwambar shekarar 1950, shekaru 10 kafin bada ‘yan Najeriya.

Malam Aminu kano yazama Shugaban jam’iyyar NEPU na kasa a shekarar 1953 har zuwa lokacin da akayi juyin mulki na farko a Najeriya.

Ya zama dan majalissar tarayya mai wakiltar Kano ta gabas karkashin inuwar jami’iyyar NEPU a shekarar 1959- 1966.

Ya samu mukamin mai tsawatarwa a majalissar hadin gwiwa.
Yayi kwamishinan Lafiya kuma dan majalissar zartawar na koli a lokacin mulkin Janaral Yakubu Gowon.

Malam Aminu Kano dashi akai ta gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga hannun farar hula azamanin Yakubu Gowon.

Dashi akai gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979.

Malam Aminu Kano shine shugaban jami’iyyar PRP kuma dan takararta na shugabancin kasa a shekarar 1979.

Yayi kaurin suna wajen kin manufofin turawa dama duk wanda zai kawowa Arewa wargi, mutum ne wanda bashi da kwadayi kuma baya bada kudi face akida zalla kawai.

Indai kajiyoshi to akan Arewane, duk kungiyoyin dayayi ko ya jagoranta to gaba dayansu zakuji na AREWA ne.

Mallam ya rasu ne ranar Asabar, 17 ga wayan Afrilun 1983.
Allah yadauki ran Malam Aminu kano aranar Asabar 17 ga watan April a shekarar 1983.

  1. Babban Asibitin Jihar Kano dake titin Zaria Road (Mal Aminu Kano Teaching Hospital)
  2. Kwalejin Ilimin Addinin Musulcin ( Legal Kano).
  3. Filin tashi da saukar jirgin Sama na Kano (Mal Aminu Kano International Airport)
  4. Makarantar Sakandire dake Goron Dutse ( Aminu Kano College)

Bayan rasuwar Mallam Aminu, Gwamnatin jihar Kano dama tarayya ta saka sunansi a jikin wasu manyan aiyuka da kuka karanta a sama.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog