Magabata: Mallam Aminu Kano “Jagoran Talakawa” ya cika shekaru 36 da rasuwa.

Mallam Aminu Kano, Jagoran Talakawa ya cika shekaru 36 da rasuwa.

Mallam ya rasu ne ranar Asabar, 17 ga watan Afirilun shekarar 1983.

Ya rasu yana dan shekara 63 da haihuwa bayan shafe kusan shekaru 40 ana gwagwarmayar siyasa don cigaba da saukaka rayuwar mallam talaka.

TALLA

Kadan daga cikin takaitaccen tarihin Malam AMINU KANO:

Marigayi malam Aminu kano yayi karatun Alqur’ani mai tsarki awajen shehun malami, malam Halilu, malam halilu shine limamin sarkin kano ABDULLAHI BAYERO a shekarar 1929 zuwa 1953.

Ansa malam Aminu kano a makarantar primary ta SHAHUCI dake kano a shekarar 1930 lokacin yana dan shekara goma da haihuwa.

Masu Alaƙa  "Abacha, Ado Bayero, Buhari da Umaru Yar'adua, ba 'yan Najeriya bane"

SIYASA:

Malam aminu kano yafara sansanar harkokin siyasa ne tun a shekarar 1943 lokacin daya taimakawa malam Sa’adu zungur suka kafa wata kungiyar siyasa mai suna kungiyar cigaban bauchi a jahar bauchi a shekarar 1946.

Malam Aminu kano da Malam Sa’adu zungur sune suka karfafa kafuwar jam’iyar NEPA wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE ASSOCIATION kafin daga baya takoma NEPU wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE UNION, ankafa jam’iyar ne a shekarar 8 ga watan 8 a shekarar 1950 kuma da mutane 8 aka kafa jam’iyar.

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.

%d bloggers like this: