Labarai

Sojojin Amurka 34 sun sami tabin kwakwalwa bayan harin da Iran ta kai musu

Kimanin Sojojin Amurka dozin uku ne suka samu rauni a kwalkwalwa sakamakon harin ramuwar gayya da kasar Iran ta kai sansanin sojin Amurka dake Iraqi, hedkwatar Sojin Amurka, Pentagon ta bayyana ranar Juma’a.

Rahoton Dabo FM wanda jaridar LegitNG Hausa ta wallafa ya bayyana cewa Kakakin Pentagon, Jonathan Hoffman, a hira da manema labarai, Jonathan yace: “Jimillar Sojoji 34 da aka gwada suna fama da rauni a kwakwalwa.”

Da farko, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa babu sojan Amurkan da aka rasa a harin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka ranar 7-8 na Junairu. Daga baya hukumomi suka bayyana cewa Sojin Amurka 11 sun jikkata.

Amma a yau, Hoffman ya ce bayan harin, an kai Sojoji 17 kasar Jamus domin jinya kuma takwas cikinsu sun dawo Amurka ranar Juma’a.

Yace: “Zasu cigaba da jinya a nan Amurka, ko a Walter Reed (Asibitin Sojojin dake kusa da Washington) ko a barikinsu.” Sauran taran da 9 da ke Jamus “na cigaba da jinya a can” Sauran 17 da suka samu rauni tuni sun samu sauki kuma sun koma aiki a Iraqi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Masana a Amurka sun gano yin azumi sau 2 a mako na kara tsawon rai da riga-kafin cututtuka

Muhammad Isma’il Makama

Za a tsige shugaba Donald Trump

Rilwanu A. Shehu

Iran tace bada gangan ta harbo jirgin da ya kashe mutane 176 ba

Dabo Online

An dauke wuta a birnin New York na kasar Amurka a karon farko cikin shekaru 42

Dabo Online

Mu muka harbi jirgin Ukraine, bisa kuskure – Jamhuriyar Iran

Dabo Online

Rikicin Amurka da Iran zai zama alfanu ga Najeriya ta fannin tattalin arziki – Masana

Faiza
UA-131299779-2