//
Wednesday, April 1

Mu ba Kwankwaso bane da za’a kwace mana zabe – Shugaban APC na Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban jami’iyyar APC na jihar Kano, Hon Abdullahi Abbas, ya bayyana cewar babu makawa sai jami’iyyarshi ta APC ta lashe zaben dan majalissar tarayya na karamar hukumar Tudun Wada da Doguwa.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin taron yakin neman sake zaben dan majalissar tarraya a karamar hukumar Tudun Wada a jiya Juma’a.

“Ranar Asabar, rana ce da babu gudu babu ja da baya, rana ce da babu kunya, komai ta-famjama-famjam.”

“Sai an bawa APC abinda yakamata a bata, sai an kyale APC taci zabenta domin mutanen Doguwa/Tudun Wada ita suka zaba. Babu wanda ya isa muci zabe ya kwace mana.”

“Mu ba Kwankwaso bane, mu ba lusaraye bane, ba dolaye ba. In munci zabenmu sai an bamu zabenmu ko da tsiy*.”

Masu Alaƙa  Da Dumi Dumi: Rarara ya saki sabuwar waka tun gabanin hukuncin kotun koli

Tini dai zuwa yanzu ana kirgen kuri’u a kananan hukumomin da ake sake zabe wadanda suka hada da Bebeji, Doguwa, Kiru, Kumbotso da Tudunwada.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020