//

Audio: Babu wani canji da Najeriya ta samu -Amaechi

dakikun karantawa

 

Faifan muryar da masu fafutukar yakin neman zaben Atiku Abubakar suka fitar ya yi nuni da maganganun ministan harkar sufurin Najeriya, Rt Hon Rotimi Amaechi yana sukar gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta.

An jiyo maganganu kamar haka: “Na rantse kasar nan ba za ta taba samun canji ba in dai ba kowa za a kashe ba, babu wani sauyi da aka samu, ba a ma san ina kasar ta dosa ba. Da gaske nake, ko za a raba kasarnan kashi goma, babu abinda zai chanza.”

A faifan muryar na biyu kuma ya yi magana kamar haka:

“Duk rubutun da ya gani, dariya yake yace “zo, zo ka gani zagina sukeyi.” Shugaban kasar baya jin maganar kowa duk abinda aka rubuta ba ya damunshi.”


Latsa alamar “Play” don jin cikakkiyar maganar

Shin muryar ta ministan ce?

Ita ce tambayar da ta shiga zukatan al’ummar Najeriya, ganin cewa ministan babban jigo ne a tafiyar shugaban kasar hasalima a yanzu shi ne jagora kuma shugaban yakin neman zaben shugaban a fafutukar da gwamnatin takeyi don cigaba da gudanar da mulkin kasar a zaben da za a gudanar a watan Fabarairun shekarar 2019.

An tutubi mai magana da yawun bakin ministan wanda ya bayyana cewa a halin yanzu babu abinda zai ce har sai sun yi bincike.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buharin dai tasha fama da samun suka daga wasu daga cikin mukarraban gwamnatin, a watanni da suka wuce ma an jiyo mai dakin shugaba Buharin , H.E Aishat Muhammad Buhari tayi kakkausar suka akan yadda gwamanatin mijinnata ke tafiyar da mulkin kasar.

Dabo FM bata tabbatar da maganar ta fito daga ministan ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog