Zinedine Zidane ya shirya komawa tsohuwar kungiyarshi ta Real Madrid tin bayan barin kungiyar a watanni 11 da suka wuce.
Tsohon dan wasan kasar Faransa dai zai maye gurbin Santiago Solari, wanda yake rikon kwarya a kungiyar tin bayan korar kociya Juleb Lopetegui.
Jaridun kasar Spaniya sun rawaito cewa a yau ne kungiyar ta Real Madrid zata bayyana dawowar dan wasan domin cigaba da horar da kungiyar.
Yanzu dai kungiyar ta Real Madrid tana mataki na 3 a teburin gasar cin kofin Firimiya na kasar Spaniya.
Kociya Solari na fuskantar kalubale tin bayan daya sha kaci a wasan zakarun nahiyar turai inda kungiyar Ajax ta doke kungiyar da ci 4 -1 a filin wasa na Santiago Bernabeu.
