Kiwon Lafiya Labarai

Yadda ake ciki game da Koronabairas a jihar Yobe

Rahotanni sunyi ta yawo cewar “an samu mai dauke da cutar Koronabairos a babban asibitin garin Potiskum dake jihar Yobe.”

Hakan na zuwa ne bayan da an kwantar da wani direban mota da ya dawo jihar Legas a babban asibitin garin Potiskum sakamakon dama da zazzabi da wahalar numfashi.

DABO FM ta tattara cewar kwamishinan lafiya na jihar Yobe, Alhaji Muhammad Lawan Gana tare da tawagarsa, sun kai ziyara babban Asibitin na Potiskum domin ganin yadda al’amura suke kasancewa.

Kwamishinan ya bayyana wa manema labarai cewa “Akwai wani direban babbar mota (Tirela) mai shekaru 30, da ya dawo daga Legas a ranar 1/4/2020.

Ya kai kanshi zuwa qaramin asibitin unguwar Dogon Zare da matsalar fama da zazzabi, tari da wahalar numfashi”

“DAga nan asibitin suka dauke shi zuwa dauke shi zuwa babban Asibitin Potiskum (General Hospital Potiskum).

Kwamishinan yace an dauki dukkanin matakan da suka dace domin kulawa da mutumin wanda bai bayyana sunanshi ba.

“An dauki duk wasu matakai, an killace shi da cikin jama’a, an dauki jininsa an tura wa hukumar NCDC dake Abuja don a yi masa gwajin Koronabairus.

Zuwa yanzu haka shi wannan marar lafiyar yana karbar kulawa ta musamman kafin sakamakon gwajin nasa ya fito”

Kwamishinan ya ce jama’a su kwantar da hankalinsu, suna iya qoqarin su wajen ganin an daqile yaduwar wannan cutar ta Koronabairus ko Covid 19.

A ranar Asabar, 4/4/2020 sakamakon gwajin mutumin ya fito, kamar yadda mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar Koronabairas na jihar, Alhaji Idi Barde Gubana ya bayyana a garin Damaturu.

Mataimakin gwamnan ya ce “Ina farin cikin shaida muku cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ba ya dauke da cutar Kwabid-19. A yanzu haka yana qara samun sauqi sosai, kuma kwana kadan za mu sallameshi ya koma gidansu.”

A cikin makon nan da muke ciki, an sake samun wanda ake zargi yana dauke da cutar a karamar hukumar Nguru bayan ya kwanta a asibitin Gwamnatin Tarayya dake Nguru.

Sai dai a yau Alhamis, kwamishinan yada labaran jihar ta Yobe, Alhaji Abdullahi Bego, ya bayyana cewar sakamakon mutumin ya nuna ba ya dauke da cutar ta Koronabairas.

Alhaji Idi Gubana ya qara da cewa “muna miqa godiyar mu ga Allah (T), sannan muna qara kira ga jama’a da su bi dokokin da Likitoci suka gindaya. Allah ya kawo mana sauqin wannan annoba”

Karin Labarai

Masu Alaka

Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta amince a bude shagunan kayyakin abinci da na magani

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Nasiru El Rufa’i ya kamu da Coronavirus

Dabo Online

Mutane 245 sun sake kamuwa da Kwabid-19, 37 a Katsina, 32 a Jigawa, 23 a Kano

Dabo Online

Gwamnatin Kano ta musanta shigar da Corona Virus cikin jihar ta filin Jirgi

Dabo Online

Da dumi-dum: Gwamna Zulum ya kulle iyakokin jihar Borno

Dabo Online

An samu mai Covid-19 na farko a Kano

Dabo Online
UA-131299779-2