Naziru Sarkin Waka
Labarai

Tana baya tana dabo: Har yanzu Sarkin Waka yana tsare bisa rashin cimma sharudai

Duk da wata Kotu a jihar Kano ta bayar da belin mawaki Naziru M Ahmad, ana cigaba da tsareshi a gidan yari.

Hakan na zuwa ne bisa dalilin rashin kammala tantance wadanda zasu tsaya masa kamar yacce Kotun ta gindaya sharudan.

Sashin Hausa na BBC ya rawaito cewa har zuwa yanzu, mawakin yana gidan Yarin Goron Dutse na jihar Kano.

Bayan zaman kotu dake unguwar Rijiyar Zaki, kotu ta ayyana bayar da belin Sarkin Waka amma bisa sharadin zai nemo wandanda zasu tsaya masa tare da cin shi tarar N500,000 hadi da jingine Fasfo dinshi na tafiya kasar waje.

A ranar Laraba ne dai jami’an yan sanda suka dira zuwa gidan mawakin dake unguwar Darmanawa a jihar Kano, suka kamashi bisa zargin karya dokar hukumar tace Fina-finai na yin kalaman batanci a waka.

“Lauyan Nazir Ahmad Barista Sadik Sabo Kurawa ya shaida wa BBC cewar da zarar sun kammla matakan tantancewar zuwa gobe Juma’a za a saki wanda suke karewa.” – BBC Hausa.

UA-131299779-2