Kwankwaso, Saraki, Atiku, Scondus

Akwai alamun cin dun-duniya tsakanin Atiku da manyan PDP

A wasu kalamai irin na bammamaki da aka jiyo gwamnan jihar Ribas, Nyseom Wike, ya furta a lokacin da yake taya shugaba Buhari samun nasara a kotu, yasa ana zargin cewa manyan PDP suna cin dunduniyar Atiku Abubakar.

DABO FM ta tattaro wani kalami daga gwamnan inda yayi nuni da cewa manyan jami’iyyar PDP suna kaiwa shugaba Buhari ziyara da daddare a sirrance.

“Kuna mamaki don na taya shugaba Buhari murna ko?,

“Na tabbata kunyi mamakin taya shugaba Buhari murna da nayi.”

“Kuna ganin baifi yimin kyau in tayashi murna da in kai masa ziyara zuwa gidanshi ba?”

Premium Times ta tabbatar da furucin gwamnan wanda yayi wajen wani zaman makoki a garin Emohua.

“Gwamnonin PDP daya suna zuwa gidanshi (Buhari) da daddare.”

Ban taba zuwa ba, kuma bazan je ba.”

Hakan zai kara tabbatar da zargin da ake yiwa wasu manyan jami’iyyar PDP na bin tafiyar Atiku domin a karbi kudadenshi kawai.

Zargin da aka fi yiwa madugun darikar Kwankwasiyya, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ana zargin cewa yaki fito da kudaden yakin neman zaben Atiku a lokacin da yakamata a fito dasu domin aiwatar da sha’anin zaben Atiku, amma sai ake ganin ya fito dasu ne lokacin zaben dan takarar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.