Taraba: An sako sakataren gwamnati da masu garkuwa suka sace

Hassan Mijinyawa, sakataren yada labaran gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya dawo gidan bayan da masu garkuwa da mutane sukayi arangama dashi akan hanyarshi ta zuwa unguwar Gembu dake karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba.

Babban mai taimakawa gwamnan jihar Taraba, Bala Dan Abu, ya bayyanawa sanarwar sako babban sakataren gwamnan a garin Jalingo, babban birnin jihar ta Taraba na yada labarai.

Ya kara da cewa ba’a biyasu ko sisin kobo ba, kuma yana cikin koshin lafiya kuma yanzu haka ma yana tare da iyalinshi.

A wanna lokaci Sakina ta roki masu garkuwan da su tausaya mata su saki mijinta da suka tafi da shi.

%d bloggers like this: