(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kano Municipal: APC batada ‘dan takarar majalisar tarayya – INEC

Karatun minti 1

Babbar hukumar zabe mai zaman kanta, INEC tace jami’iyyar APC batada ‘dan takarar majalisar tarayya a karamar hukumar birnin jihar Kano.

Biyo bayan umarnin wata kotu a jihar ta Kano, hukumar ta INEC ta cire sunan Sha’aban Ibrahim Sharada, mataimaki na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari a fanni kafofin sadarwa.

A ranar 15 ga watan Janairun 2019, kotu karkashin alkalancin mai shari’a Justice Sa’adatu Ibrahim, ta baiwa tsohon shugaban karamar hukumar Birni da kewaye, Hon Muntari Ishaq nasara a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a shekarar data wuce.

Mai magana da yawun hukumar ta INEC shiyar jihar Kano, Malam Lawan ya bayyana cire sunan Sha’aban bisa bin umarnin kotu kuma yace har yanzu jami’iyyar da APC bata bada sunan wanda zai maye gurbin Sha’aban ba.

Duk da hakan bazai yiwuba sai in kotu tace a karbi sunan wanda jami’iyyar ta kawo saboda wa’adadin da hukumar ta bayar na bada ‘yan takarkaru ya wuce, a cewar Malan Lawan.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog