Siyasa

Kano: Ni yakamata a zaba – Muhammad Abacha

Muhammad Abacha, ‘da ga tsohon shugaban kasar ta Najeriya, Gen Sani Abacha yace jihar Kano shi kadai take bukata.

Abacha, yace zai farfado da harkar masana’antu data dade da faduwa a jihar Kano, zai kokari wajen kawar da shaye-shaye da kuma rashin aikin yi.

Dan takarar gwamnan na jami’iyyar APDA, ya alkauranta cewa bazai zuba ido ya kuma bari ayi sama da fadi da dukiyar al’ummar ba, zai tabbatar da an kashe kowacce kwandala a duk inda ya dace.

“Karuwar rashin aikin yi a jihar nan abune da yake daga mana hankali, abin kullin karuwa yake kuma duk shekara sai an yaye dalibai daga makarantun gaba da sakandire.”

Kano gari ne dake bukatar gwamnan da zai janyo hankalin masu zuba jari ba wanda zai kashe harkar kasuwanci a jihar bama baki daya, gari ne da aka sani da kasuwanci, burinmu shine farfado da kuma dawowa da jihar Kano kambunta na ja gaba a harkar kasuwancin Najeriya

Muhammad Abacha dai ya fito takarar neman gwamnan jihar Kano har sau uku, kuma yasha alwashin aiwatar da aiyukan daya dauko a cikin kwana dari idan al’ummar jihar Kano suka kada masa kuri’arsu.

Karin Labarai

Masu Alaka

Matar Aure ta zabgawa Mijinta Guba a jihar Kano

Dabo Online

Bincike ya nuna Ƴan Majalisar Tarayya na Kano ɗumama kujera suke a Habuja

Muhammad Isma’il Makama

Ba’a ga Sarkin Kano Sunusi ko wakilinshi a taron rantsar da Ganduje ba

Dabo Online

Anyi suya an manta da Albasa – Hon Kofa ya tashi a tutar babu

Dabo Online

‘Yan sanda sunyi alkawarin kama duk masu hannu a yiwa Pantami ihun ‘Bamayi’

Muhammad Isma’il Makama

Kano: In bidiyon da aka ganmu gaskiya ne a ina aka ga mun yaga takardar zabe? – Murtala Garo

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2