Yadda Boko Haram ta yi wa manoma da masunta 66 yankan Rago a Borno

dakikun karantawa

Rahotanni sun bayyana yadda kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram ta yi wa wasu manoma wadanda yawancin manoman shinkafa ne yankan rago garin Zamarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno.

Rahotannin sun ce mayakan sun yanka manoman a kauyen Koshebe, kimanin kilomita 20 zuwa birnin Maiduguri.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa adadin wadanda aka yanka sun kai mutum 66 wadanda suka hada da manoman shinkafa da kuma masunta, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar.

DABO FM ta tattara cewa aikin ta’addancin ya faru ne da safiyar Asabar, kamar yadda wasu mazauna garin suka tabbatar mata.

Bayanan da aka bayar ya nuna cewa mayakan sun yanka manoman ne bayan sun daddauresu a lokacin da suke girbin shinkafa.

Zuwa yanzu rahotanni sun tabbatar da samun gawarwakin mutum 43 inda har yanzu ana cigaba da gano sauran gawarwakin.

Wani wanda ya kubucewa hari mai suna Abdullahi Abdullahi ya ce; “Mayakan sun shigo garin su kimanin 100 a kan babura da yawansu ya kai 50.”

Kazalika wani mazaunin kauyen da ya bayyana sunansa, Haruna Isa, ya ce ya ga wasu ma’aikatan sa kai da jami’an tsaro suna dauke wasu gawarwakin wadanda aka kashe zuwa wani asibiti a jiya da yamma.

“Eh tabbas jiya mayaka sun afka wa masunta a kauyen Koshobe, bansan adadin mutanen da aka kashe ba, sai dai na ga jami’an CJTF suna daukar gawarwaki zuwa Maiduguri.”

A nashi bangaren shugaba Buhari, kamar kullin, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda lamarin ya faru ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan manoman.

Sanarwa ta fito daga babban mataimakin shugaban a fannin yada labarai, Mallam Garba Shehu.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog