Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Labarai

Ganduje ya rufe wani gidan renon yara mara rijista dake unguwar da kabilun jihar suke zaune

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wani gidan yara mai sunan Du Merci Orphanage dake a unguwar Noman’s Land, Sabon Gari ta karamar hukumar Fagge.

DABO FM ta tattara cewa unguwar ta kasance mafiya yawan masu zama a unguwar ‘yan kabilar Ibo ne.

A matakin da gwamnatin ta dauka, tace ta rufe gidan ne bisa rashin rijista. wanda ya shafe shekaru 25 ana gudanar dashi.

Ofishin mai bawa gwamna shawara a harkokin walwalar Mata da kananan Yara, Hon Fatima Abdullahi Dala, ne ya bayyana rufe gidan a yau Laraba.

A wata sanarwa da ofishin mai bawa gwamna shawara a harkokin walwalar Mata da kananan Yara, Hon Fatima Abdullahi Dala, ta fitar, tace gwamnatin ta rufe gidan ne bisa gudanar dashi har tsawon shekaru 25 ba tare da rijista ba.

“An gano cewar akwai takwaran gidan dake a jihar Kano duk da sun shafe tsawon shekaru 25 ba tare da samun sahalewa daga gwamnatocin jihohin guda biyu ba.”

“Daga abinda muka samu daga hukumomi, sun tabbatar mana da cewa basu da rijista. Wannan babban lamari ne sosai ace gidan marayu yana gudana har tsawon shekaru 25 ba tare da rijista ba.

Hon Fatima Dala tace lallai a bayyana yake cewar gidan ya shiga cikin zargi musamman akan abinda ke faruwa da kananan yara a jihar.

“Har yanzu muna cikin dimuwa akan yaran mu da aka sace da wandanda aka ceto, saboda haka gwamnatin Kano baza tayi wasa da duk wani abu na zargi kamar wannan gidan Du Merci Orphanage wanda ka iya jefa yaranmu cikin wahala.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ganduje, Sarki Sunusi sun jagorancin daurin auren Zaurawa 70

Dabo Online

An shawo kan rashin jituwar Ganduje da Sarki Kano Sunusi

Dabo Online

Muna aiki ta karkashin kasa domin sasanta Sarki Sanusi da Ganduje -Shekarau

Muhammad Isma’il Makama

Yadda Ganduje ya taka rawa a taron kaddamar sabon garejin gyaran motoci na mata da maza

Dabo Online

Kano: Ganduje yana yunkurin rage darajar sarautar Sarki Sunusi

Dabo Online

Ganduje ya kaddamar da kwamitin don fara shirin Ruga a Kano.

Dabo Online
UA-131299779-2