//
Friday, April 3

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tsohon dan majalisar jamhuriya ta biyu, Junaid Muhammed ya bayyana Sarkin  Kano, Muhammadu Sanusi II yayi zawarcin kujerar mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari yake kwance a asibiti a birnin London.

Majiyar Dabo FM ta bayyana Junaid na cewa: “Sanusin ya nemi Osinbajo ya bashi kujerar mataimakin shugaban kasa idan Buhari ya rasu, tinda shine shugaban babban bankin kasa.” A rahoton jaridar TheCable.

A shekarar 2017 dai aka kwantar da shugaba Buhari a asibitin birnin London wanda a lokacin ake ta rade radin rasuwar sa.

Junaid ya kara da cewa “Sanusi saida yabi shugabannin kudu maso yamma domin suyi masa hanyar samun goyon baya don cimma burin sa, domin a tinanin sa tabbas Buhari bazai rayu ba, da wani shugaba ne ba Buhari ba da yayi maganin sa.”

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020