Labarai

Tsananin sanyi da hazo ya tilasta mutane zaman gida a jihar Jigawa

Yanayin sanyi da hazo, a ranar Asabar ya sanya mutane a garin Dutse na jihar jihar Jigawa zaman gida, kamar yacce kamfanin dillancin labaran Najeriya ya tabbatar.

Wakilin kamfanin, wanda ya zazzaga zuwa guraren da suka kasance masu cunkoso, inda wuraren suka kasance babu mutane.

Bayan zantanwa da wani matukin tasi, Malam Yunusa Minari, ya shaida cewa ya shafe kusan awanni biyu a tasha babu fasinja.

Mallam Yunusa ya bayyana cewa yana cika motarshi a kan titin Dutse zuwa Birnin Kudu a minti 30, sai dai yace bayan shafe awanni biyu yana jira, fasinjoji biyu kacal ya samu.

Haka zalika anga dusashewar mutane a titin Hakimi da ya kasance mafi cunkoso, sai dai anga ‘yan tsirarun mutane a teburan masu shayi.

Wata matar aure, Hauwa Abdullahi, ya bayyana sanyin wannan lokacin a matsayin wanda yayi tsanani sosai wanda hakan yayi sanadiyyar dena zuwan makarantar ‘ya’yanta.

Tace ‘ya’yanta nata basa iya shiga cikin sanyin dake hade da hazo, shiyasa ta yanke dalilin sun dakatar da zuwa makarantar a yanzu.

Duk dai a cikin garin Dutse, Titin Sani Abacha, babu mutane sai ‘yan tsirarun motoci dake wucewa kowanne da fitila a kunne a dalilin duhu.

Karin Labarai

UA-131299779-2