1
‘Yan ta’adda masu garkuwa da mutane sun sace matar dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Miga, dake jihar Jigawa, Wanarabul Haruna Dangyatum.
Rahoton da Dabo FM ta hada ya bayyana cewa kakakin rundunar yan sanda na jihar, Abdu Jinjire ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce yan bindiga 3 ne suka dira kauyen Dangyatum dake karamar hukumar Jahun.
Ya kara da cewa sun dauke matar dan majalisar dokokin mai suna Zarau Haruna ne a ranar Asabar da misalin karfe 4 na asuba a kauyen Dangyatum.
Rundunar ‘Yan Sandan tace tini sun shiga bincike mai tsauri na bin sahun barayin mutanen kuma nan gaba kadan zasu binciko su.
